2019-09-22 15:44:50 cri |
Sanawar da majalisar ministocin kasar ta fitar a jiya, ta ce kwamitin ya kunshi mutane 7, ciki har da alkalin kotun koli da wakilai daga ma'aikatu daban daban, da kuma wasu lauyoyi 2 masu zaman kansu.
Bisa dokar kafa kwamitin bincike na 1954 ta kasar, kwamitin na da dukkan iko na gudanar da binciken da ya kamata.
Ana sa ran kwamitin ya kammala aikinsa cikin watanni 3, sannan ya na da damar tsawaita lokacin idan bukatar hakan ta taso.
A watan Augusta ne kwamitin mulkin soji na wucin gadi da kungiyar adawa, mai rajin tabbatar da sauyi da 'yanci, suka rattaba hannu kan yarjejeniyar kafa mulkin hadin gwiwa na wucin gadi a kasar.
Bisa yarjejeniyar, za a kafa kwamiti mai zaman kansa da zai yi bincike kan rikicin da ya auku ranar 3 ga watan Yuni da sauran wasu rikice-rikice. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China