Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sudan ta kudu za ta amince da yarjejeniyar kayyade cinikin makamai ta kasa da kasa a hukumance
2019-09-26 11:15:34        cri
Sudan ta Kudu ta sanya hannu kan wata yarjejeniya da cibiyar takaita yaduwar kananan makamai ta haramtacciyar hanya ta yankin manyan tabkuna da kahon Afrika, da nufin karfafa amincewa da yarjejeniyar kasa da kasa ta kayyade cinikin makamai.

Shugaban hukumar kula da tsaron al'umma da takaita yaduwar kananan makamai ta kasar, Andrew Kuol Nyuon, ya ce hukumar na gudanar da gangami a fadin kasar, da nufin wayar da kan manyan masu ruwa da tsaki, kan bukatar goyon bayan yarjejeniyar da ta haramta kwararar kananan makamai ba bisa ka'ida ba.

Andrew Nyoun, ya alakanta kaso 70 na mace-macen da ake samu a kasar, da kwararar kananan makamai ba bisa ka'ida ba, yana mai cewa, a matsayinsu na hukuma, sun kuduri niyyyar yin nasara wajen takaitawa da rage kananan makamai a kasar.

Ya ce yarjejeniyar kayyade cinikin makaman, wani bangare ne na yarjejeniyar Nairobi, wadda kasashen yankin manyan tabkuna da kahon Afrika da kasashen dake makwabtaka da su suka amince da ita a shekarar 2014. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China