Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwamitin harkokin waje na majalisar wakilan jama'ar Sin ya fidda sanarwa kan daftarin dokar hakkin bil Adama da dimokuradiyya a Hong Kong na shekarar 2019 da Amurka ta zartas
2019-09-27 14:15:13        cri
Jiya Alhamis, kwamitin harkokin waje na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya fidda wata sanarwa dangane da daftarin dokar hakkin bil Adama da dimokuradiyya a yankin Hong Kong na kasar na shekarar 2019 da kwamitin harkokin waje na majalisar dokokin kasar Amurka ya zartas.

Cikin sanarwar, kwamitin ya bayyana cewa, a ranar 25 ga wata, majalisar dattawa da majalisar wakilan kasar Amurka, sun yi biris da gargadin da kasar Sin ta yi sau da dama, inda suka zartas da daftarin dokar hakkin bil Adama da dimokuradiyya kan yankin Hong Kong na shekarar 2019, domin tsoma baki cikin harkokin gidan kasar Sin bisa hujjar kiyaye hakkin bil Adama da tabbatar da dimokuradiyya. Kwamitin harkokin waje na majalisar wakilan jama'ar Sin ya yi Allah wadai da kakkausan harshe kan wannan batu.

Hong Kong wani yanki ne na kasar Sin, harkar yankin ta zama harkar cikin gidan kasar Sin. Kana, aikin kare zaman karko a wannan yanki, aiki ne na dukkanin jama'ar kasar Sin, bai kamata kasashen ketare su yi yunkurin canja makomar yankin Hong Kong ba ta hanyar matsawa kasar Sin lamba. Dukkan ayyukan da suka shafi bata ikon mallakar kasar Sin, ko kuma kawo barazana ga ikon gwamatin kasar da babbar dokar kasar, ko shakka babu ba za su ci nasara ba.(Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China