Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban sakataren kungiyar SCO ya ba da sanarwa kan yanayin Hong Kong
2019-09-24 10:50:46        cri
Babban sakataren kungiyar hadin kai ta Shanghai SCO ya bayar da sanarwa jiya 23 ga wata kan yanayin da ake ciki a yankin Hong Kong, inda ya bayyana cewa, mambobin kungiyarsa na adawa da yadda wasu kasashen waje ke tsoma baki a harkokin yankin Hong Kong na kasar Sin.

Sanarwar ta ce, kungiyar SCO na martaba dokokin kasa da kasa, ya kamata a martaba kundin tsarin mulkin MDD, musamman ma ka'idojin daina tsoma baki a harkokin cikin gidan juna, girmama ikon mulki da cikakken yankin kasashen juna, da ma kiyaye muradun kasa da kasa.

Don haka, kungiyar ta yi kira ga wasu kasashen waje, da su yi watsi da duk wani yunkurin da zai tsananta halin da yankin Hong Kong ke ciki, da daina kawo cikas ga aikin maido da oda da kwanciyar hankali a yankin.(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China