2019-08-09 09:20:55 cri |
Mr. Nabasu ya bayyana hakan ne, yayin wani taron karawa juna sani game da kare ingancin abinci, wanda ya gudana a jihar Nasarawa dake shiyyar tsakiyar kasar, yana mai cewa a duk shekara a kasar wadda ta fi sauran kasashen Afirka yawan al'umma, ana samun bullar nau'ikan cututtuka kimanin 90,000 masu nasaba da cin abinci maras kyau.
Ya ce sau da yawa abinci na gurbata ne yayin da ake sarrafa shi, ko kuma ta hanyoyin alkinta shi. Domin shawo kan wannan matsala, jami'in ya ce ya zama wajibi hukumomin da lamarin ya shafa, kamar SON da hukumar NAFDAC, su kara azama wajen tabbatar da cewa, ana aiwatar da matakan kare ingancin abincin da al'ummar kasar ke amfani da shi a dukkanin matakai. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China