2019-07-24 09:23:57 cri |
Mataimakin kakakin babban magatakardar MDD Farhan Haq, ya ce sakamakon fama da tashe tashen hankula da suka addabi yankin arewa maso gabashin Najeriya a tsawon kusan shekaru 10, al'ummu da yawansu ya kai miliyan 7 na fama da kalubalen rayuwa, ciki hadda kimanin mutane miliyan 3 dake fuskantar karancin abinci.
Farhan Haq, ya bayyana hakan ne a jiya Talata, yana mai cewa, tashe tashen hankulan sun kuma raba mutane kimanin miliyan 1 da duba dari 8 da gidajen su, yayin da wannan adadi ke karuwa, a gabar da dakarun sojojin kasar ke dauki ba dadi da mayakan kungiyoyi masu dauke da makamai.
To sai dai kuma duk da wannan kalubale na tsaro, jami'in na MDD ya ce, kungiyoyin bada agajin jin kai sun kai ga tallafawa mutane sama da miliyan 2 a wannan yanki. Haq ya ce a shekarar nan ta 2019, ana bukatar kudade da yawansu ya kai dalar Amurka miliyan 848, domin tallafawa mutane miliyan 6.2 a kasar, ko da yake kawo yanzu adadin da aka samu bai wuce kaso 33 bisa dari ba.
A hannu guda kuma, Mr. Haq ya ce ana bukatar kudade da yawansu ya kai dalar Amurka biliyan 1.3 a shekarar ta bana, domin gudanar da ayyukan jin kai a shiyyar da Najeriyar take, ko da yake kawo yanzu, kaso 20 bisa dari na kudaden aka kai ga samu. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China