Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ambaliyar ruwa ta kashe daliban jami'a 4 a arewa maso gabashin Najeriya
2019-08-07 09:14:20        cri
Ambaliyar ruwa data afkawa jami'a a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya ta yi sanadiyyar hallaka wasu dalibai 4, hukumar gudanarwar jami'ar ne ta bayyana hakan a jiya Talata.

Lamarin dai ya faru ne a jami'ar Abubakar Tafawa Balewa dake garin Gubi a jahar Bauchi dake shiyyar arewa maso gabashin Najeriya da yammacin ranar Litinin, akwai wasu dalibai da dama da suka bace yayin da wasu daliban 7 sun samu raunuka, kamar yadda mataimakin shugaban jami'ar Muhammed Abdulaziz ya bayyana a taron manema labarai.

A cewar Abdulaziz, hukumar gudanarwar jami'ar ta sanar da rufe ta nan take domin nuna juyayi ga wadanda hadarin ya rutsa da su. Za'a sake bude jami'ar a ranar 19 ga watan Augasta.

Wani mamakon ruwan sama da aka sheka kamar da bakin kwarya a ranar Litinin yayi sanadiyyar haddasa ambaliyar ruwa lamarin da ya haifar da karyewar gada wacce ta hade dakunan kwanan dalibai da cikin jami'ar.

Mataimakin shugaban jami'ar ya ce, daliban suna kokarin komawa dakunan kwanansu ne a daidai lokacin da ake sheka ruwan saman a daren ranar Litinin inda gadar data hada harabar azuzuwan karatu da dakunan kwanan daliban ta rufta inda nan take daliban suka nitse cikin ruwa.

Wata majiya daga yankin ta shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa dalibai da dama suna kokarin tsallaka gadar ne wacce ta rufta a sanadiyyar ambaliyar ruwan. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China