Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya ta haramta kungiyar IMN a hukumance
2019-07-31 09:40:01        cri
Babban sifeton 'yan sandan Najeriya Mohammed Adamu, ya bayyana cewa, an haramta kungiyar 'yan uwa musulmi (IMN) wadda aka fi sani da Shi'a a hukumance, da ma shirya duk wata zanga-zanga a fadin kasar.

Da yake karin haske yayin wani taron manema labarai a Abuja, fadar mulkin kasar ta Najeriya, Adamu ya ce, daga yanzu duk wanda ya yi alaka da kungiyar ko ya yayata manufofin ta, za a dauki shi tamkar dan ta'adda kuma makiyin kasa.

Jami'in ya ce, ayyukan kungiyar suna kawo barazana ga tsaron kasa, da doka da oda da zamantakewar addinai da jin dadin jama'a, da zaman lafiya da shugabanci na gari da ma 'yanci da martabar Najeriya.

Haramta kungiyar 'yan shi'a da mahukuntan Najeriya suka yi, ya biyo bayan jerin zanga-zanga da magoya bayan kungiyar suka shirya, inda suke neman a saki jagoransu Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da mai dakinsa da ake tsare da su tun a shekarar 2015.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne, wata babbar kotun tarayyar dake Abuja, ta ba da umarnin cewa, ya kamata a haramta kungiyar, biyo bayan bukatar hakan da gwamnatin tarayya ta gabatar mata. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China