Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An shirya liyafar ban gajiya ta cikon shekaru 92 da kafa rundunar sojoji a ofishin jakadancin Sin dake Najeriya
2019-07-30 19:20:55        cri
A daren jiya Litinin, babban kanal na sojin kasar Sin, kuma babban jami'in ofishin jakadancin kasar Sin dake Najeriya wanda ke kula da harkokin soji Liu Yongxuan, ya shirya liyafar ban gajiya a birnin Abuja, don murnar cika shekaru 92 da kafa rundunar sojojin 'yantar da jama'ar kasar Sin.

Jakadan kasar Sin dake Najeriya Zhou Pingjian, da duk jami'an diplomasiyya dake aiki a ofishin, da mataimakin ministan harkokin cikin gida na Najeriya, da hafsan-hafsoshin sojojin sama, da jami'an ofisoshin jakadancin kasashen ketare dake Najeriya, da kuma wasu wakilan kamfanoni da hukumomi na kasar Sin dake Najeriya da yawansu ya kai kimanin 300 sun halarci liyafar.

A yayin jawabinsa, babbar kanal din ya ce, ko da yaushe kasar Sin da kasashen Afirka, suna da kyakkyawar makomar bai daya. A gun taron dandalin tattaunawa karo na farko game da batun zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin Sin da Afirka, wanda aka shirya a ranar 15 ga wata a nan birnin Beijing, wanda aka mayar da hankali kan sabbin matakan hadin kai da za a dauka a tsakanin bangarorin biyu a fannin, kana kuma aka samu manyan nasarori.

Baya ga haka, Liu ya bayyana cewa, a cikin 'yan shekarun baya, ana ta karfafa mu'amala da hadin kai a tsakanin shugabannin soja na kasashen Sin da Najeriya. A cewar Liu, kasar Sin na kokarin ciyar da dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu gaba. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China