2019-07-19 15:23:53 cri |
An gabatar da takardar zuba jari kan sabbin kamfanoni da ake ganin suna da makoma a duniya na shekarar 2019 jiya Alhamis, inda aka bayyana cewa, a cikin shekaru 3 da suka gabata, kashi daya bisa hudu na yawan wadannan kudade da aka zuba kan wannan fanni sun fito ne daga kasar Sin. Ya zuwa karshen watan Mayu na bana, yawan kudaden da aka yi rajistar su a wannan fanni a kasar Sin, ya wuce kudin Sin RMB triliyan 1, wanda yawansu ya kai guda 7055, hakan ya sa yawan irin wadannan kudade da kasar Sin ta zuba kan irin wadannan kamfanoni ya zarce na Amurka.
Masana sun bayyana cewa, idan aka hada kudi da fasaha, hakan zai kara zurfafa gyare-gyare a bangaren samar da kayayyaki a kasar Sin, da kuma daga matsayin tsarin tattalin arzikin kasar. Ta haka, aikin sana'ar zuba jari kan sabbin kamfanoni dake da makoma, zai kara bunkasa cikin sauri. (Amina Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China