Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin zata kafa tawagar masu sanya ido don tabbatar da ingancin magunguna
2019-07-19 10:03:02        cri

Gwamnatin kasar Sin za ta kafa tawagar musamman wadda ta kunshi kwararrun masana hada magunguna a matakan gwamnatin tsakiya da larduna, domin su tsaurara aikin sanya ido da kuma tabbatar da bin dokar kiyaye ingancin magunguna, wanda ya hada har da na'urorin hada magunguna da na kayan kwalliya.

Wata sanarwa daga babban ofishin majalisar gudanarwar kasar Sin ta ce, hukumomin kula da magunguna ne suka amince da wannan matakin, kana tawagar masu sanya idon za su gudanar da ayyukansu ne bisa tsarin dokoki, da bincika wuraren hada magunguna, da yadda ayyukan binciken hada magungunan ke gudana, da kuma tabbatar da cewa ko kamfanonin dake hada magungunan suna gudanar da ayyukansu bisa tsarin mafi inganci, kana za su binciko dukkan wasu haddura dake tattare da ayyukan hada magungunan.

Za'a kara azama wajen tabbatar da binciken yadda ake harhada alluran rigakafi da sauran magunguna wadanda ka iya haifar da barazana ga lafiyar jama'a, kana za'a kara tsaurara matakan bincike a wadannan fannoni.

Babbar majalisar dokokin kasar Sin ta amince da dokar kula da alluran rigakafi a watan Yuni. Dokar ta nemi a binciki dukkan ayyukan hada magungunan, kana ta nemi a dauki tsauraran matakan ladaftarwa ga dukkan wadanda aka samu da hannu wajen saba dokokin. Dokar zata fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Disambar shekarar 2019. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China