Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masana: Tattalin arzikin Sin na samun ci gaba cikin karko
2019-07-18 14:06:10        cri
Rahoton rabin shekara da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta gabatar a kwanakin baya ya nuna cewa, a farkon watanni 6 na bana, tattalin arzikin kasar ya karu da kashi 6.3% bisa makamancin lokacin bara, inda yake cikin wani yanayi na karko, tare da samun ci gaba. Ganin haka ya sa wasu masana na kasashe daban daban ke ganin cewa, ko da yake ana fuskantar wani yanayi na rashin tabbas a duniya, tattalin arzikin Sin na samun ci gaba cikin karko, tare da samar da gudunmowa ga yunkurin raya tattalin arzikin duniya.

A cikin masanan, Christiane Rusche, wanda ya zo daga cibiyar nazarin tattalin arziki ta Cologne na kasar Jamus, ya ce wasu al'amuran da suka hada da takaddamar ciniki, da yadda kasar Birtaniya ke janye jikinta daga kungiyar tarayyar Turai EU, da tsanantar yanayin siyasa a yankin gabas ta tsakiya, da dai sauransu, sun haifar da illa ga ci gaban tattalin arzikin duniya. Duk da haka, tattalin arzikin kasar Sin ya ci gaba da samun karuwar da ta zarce kashi 6%, tare da nuna wani yanayi na yakini. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China