Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Manyan kusoshin Sin da Afirka sun tattauna batun karfafa hadin gwiwa a fannin noman shinkafa
2019-07-18 14:12:11        cri
Shinkafa tana da muhimmanci a harkar noma ta kasashe da yawa dake nahiyar Afirka, amma wasu daga cikinsu ba su iya samar da isashen shinkafar da suke bukata, abin kawai da za su iya yi shi ne dogaro kan shigar da shinkafa daga ketare. Don daidaita wannan yanayin da ake ciki, a jiya Laraba, wasu jami'ai da masana na kasashen Afirka da na kasar Sin sun halarci wani taro a birnin Beijing na kasar Sin, inda suka tattauna damar gudanar da hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, a fannin noman shinkafa.

A wajen taron, darektan sashen aikin noma na yankin arewa maso yammacin kasar Najeriya, Mathew Owolabi, ya ce, aikin noman shinkafa a Najeriya na fuskantar matsalolin da suka hada da rashin kudi, da kasa samar da isashen hatsin da ake bukata, da dai sauransu. Don haka yana fatan samun damar karfafa hadin gwiwar da ake yi tsakanin Najeriya da Sin, a fannin horar da ma'aikata, da kuma wasu fannoni. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China