Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya gana da babban jami'in Liberia
2019-07-18 14:10:25        cri
Li Zhanshu, shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, ya gana da Albert Chie, shugaban wucin gadi na majalisar dattawa ta kasar Liberia, a jiya Laraba, a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Yayin ganawar, Mista Li ya ce, a ganin kasar Sin, yadda kasar Liberia ta kafa wata doka don tabbatar da matsayarta kan manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, abin yabawa ne. A karkashin jagorancin ra'ayi daya da shugabannin kasashen 2 suka cimma, majalisar wakilan jama'ar kasar Sin za ta yi kokarin kafa wasu dokoki don samar da tabbaci ga ayyukan aiwatar da tsarin hadin kai da aka tabbatar da shi a taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasashen Sin da Afirka da ya gudana a birnin Beijing a bara, da aiwatar da shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya", da karfafa hadin gwiwar kasashen 2.

A nashi bangare, Albert Chie ya ce, kasar Liberia tana tsayawa tsayin daka kan manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, kana tana fatan yin amfani da damammakin shawarar " Ziri daya da Hanya Daya", da ci gaban hadin kan Afirka da Sin, don kara musayar ra'ayi tsakanin hukumomin kafa dokoki na kasashen 2, da karfafa hadin gwiwarsu a bangarori daban daban. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China