2019-07-17 11:14:46 cri |
Jami'in ya bayyana hakan ne yayin taron tallafawa yankin karo na 7 da ya gudana a Hotan, dake kudancin yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa.
Wang ya ce, shirin zai taimaka wajen bullo da wata sabuwar hanyar raya yankin, da ba da gudummawa ga ci gaban tattalin arziki da inganta rayuwar jama'a, zai kuma taimaka wajen hada kan mazauna yankin baki daya.
Tun a shekarar 1997 ne dai kasar Sin ta fara aiwatar da shirin taimakawa yankin Xinjiang, inda sauran yankunan kasar ke tattara kudade don taimakawa yankin da tura ma'aikata da kwararru don su yi aiki su kuma rike mukamai na wasu lokuta a wurin.(Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China