Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanan Amurka da dama sun nuna adawa kan nuna kiyayya ga kasar Sin
2019-07-04 13:58:01        cri
Wasu kwararru da masana gami da jama'a daga bangaren kasuwanci sama da dari na Amurka, ciki har da tsohuwar mataimakiyar sakataren harkokin wajen Amurka mai kula da harkokin yankin gabashin Asiya da tekun Pasifik Susan A. Thornton, da tsohon jakadan Amurka dake kasar Sin J. Stapleton Roy, gami da shehun malami Ezra Vogel daga jami'ar Harvard, sun aikewa shugaba Donald Trump da majalisar dokokin kasar, inda suke adawa da manufar yin fito na fito da kasar Sin..

Wasikar mai taken "China Is Not An Enemy" a turance, wato "Sin ba abokiyar gaba ba ce" an wallafa ta ne a jiya Laraba a jaridar Washington Post, inda ta bayyana cewa, matakan da gwamnatin Amurka ta dauka na kara lalata dangantakarta da kasar Sin, kuma kwararrun na ganin cewa, tsamin dangantakar kasashen biyu bai dace da moriyar Amurka da ma duniya baki daya ba.

Wasika ta kara da cewa, nuna kiyayya ga kasar Sin da Amurka ta ke yi, ba zai kawo cikas ga habakar tattalin arzikin Sin ba, kana ba zai hana bunkasuwar kamfanonin Sin dake sassan duniya ba, duk da haka ma Sin na kara taka muhimmiyar rawa a harkokin kasa da kasa.

Kwararru da masana gami da tsoffin manyan jami'an gwamnatin Amurka masu tarin yawa ne suka sa hannu kan wasikar, yawancinsu fitattu ne a bangarorin diflomasiyya da ilimi da siyasa da kasuwanci da aikin soja.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China