Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan mutanen da suka mutu a kifewar kwalekwale a Najeriya ya kai 12
2019-07-03 09:42:24        cri

Yayin da hukumar ba da agajin gaggawa ke ci gaba da gudanar da aikin ceto, mutanen da suka mutu sakamakon kifewar wani kwalekwale a tekun jihar Legas dake Najeriya ya karu zuwa 12.

Wasu jami'an yankin sun tabbatar da cewar, an samu karin gawarwakin mutane 5 a farkon wannan rana a yayin da hukumomin tsaro da ma'aikatan ceto ke ci gaba da gudanar da ayyukansu. Ya zuwa ranar Litinin, gawarwaki mutane 7 ne aka samu, wanda ya hada har da wata mace mai juna biyu, yayin da wasu mutane 10 kuma sun bace.

Kwalekwalen wanda ke da karfin daukar fasinjoji 20 mai karfin inji na horsepower 60, ya nitse ne a tsakiyar teku bayan da igiyar ruwa ta kada shi a daren ranar Asabar a kan hanyarsa daga Badore-Ijede zuwa Ikorodu dake jihar Legas.

Oluwadamilola Emmanuel, janar manajan hukumar kula da tekun jihar Legas ya ce, a halin yanzu gawarwakin mutane 5 ne ake ci gaba nema.

Emmanuel ya ce, a bisa binciken da aka gudanar game da musababbin kifewar jirgin ruwan, an gano cewa, matsalar rashin ingantaccen gani da matukin jirgin ke fama da shi da kuma rashin sanya rigar kariya daga bangaren fasinjojin su ne suka haddasa hadarin.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China