Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Nijeriya sun kashe tsageru 15 a jihar Zamfara
2019-06-29 15:11:41        cri

Rundunar sojin Nijeriya, ta ce an kashe 'yan bidiga 15 yayin wani artabu tsakaninsu da sojoji a jihar Zamfara dake arewa maso yammacin kasar.

Kakakin rundunar sojin Lt. Abayomi Oni-Orisan, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, dakarun dake aiki a yankin, sun yi artabu mai tsauri inda suka fuskanci turjiya daga tsagerun masu dauke da manyan makamai, a ranar Alhamis a lardin Dansadau na jihar.

Sai dai ya ce daga bisani, sojojin sun ci karfin tsagerun, inda wasu daga cikinsu suka tsere da raunikan harbi.

Abayomi Oni-Orisan, ya ce dakarun sun kai samame ne maboyar tsagerun da suka addabi yankin, dake dajin Madada na lardin Dansadau, na yankin karamar hukumar Maru ta jihar.

A cewar kakakin, an kashe soja guda, sannan wani dan kungiyar sintiri ya samu mummunan rauni.

Hukumomin tsaron kasar sun bayyana cewa, an dorawa dakarun nauyin ci gaba da fatattakar tsagerun daga yankin, kana an ba su umarnin lalata sansanoninsu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China