Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kociyan Najeriya ya ce tawagar 'yan wasan kungiyarsa sun samu ci gaba a gasar kofin duniya
2019-06-23 17:07:54        cri

Babban mai horas da 'yan wasan kwallon kafan mata ta Najeriya Thomas Dennerby ya ce, kungiyar 'yan wasansa ta nunawa duniya cewa ta samu kyautatuwa matuka, duk da cewa ba ta yi nasara ba a zagaye na 16 na gasar cin kofin kwallon kafan mata ta duniya ta hukumar FIFA.

"Mun nunawa duniya cewa kungiyar wasan Najeriya ta samu gagarumin ci gaba." Dennerby ya bayyana hakan ne ga taron 'yan jaridu.

"Ba lallai ne a gamsu da yadda al'amarin ya kasance ba, amma ya kamata a fahimci daga inda muka fito. Har yanzu ba mu shirya ba. Har yanzu muna kokarin inganta kungiyar wasan ta yadda har suka samu damar taka leka kamar haka, kuma yana da muhimmanci a gane cewa a nan gaba kungiyar wasan za ta ba da mamaki matuka, ba za'a yanke hukunci saboda wani karamin kuskure ba."

"Mun taka leda a rukunin wasa na 4, 12 da na 14, yayin da a yanzu muke rukuni na 38. Ya kamata mu fahimci daga inda muka taso kuma ina muka dosa. Wani abin farin ciki shi ne, har yanzu muna ci gaba da samun damammaki, kuma a yau ma mun samu wata damar a kan Jamus. Muna bukatar mu kara samun yawan kwallaye. Lamarin ya shafi yin aiki tukuru a kullum.

"Ina alfahari da irin ci gaban da kungiyar wasan ta samu, kuma za mu kai matakin karshe, amma ban gamsu ba kuma ba na farin ciki a fitar da mu a zagaye na 16".(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China