Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya ta ce dakarun hadin gwiwar kasashen Afrika sun kashe mayakan Boko Haram 42
2019-06-23 15:12:41        cri

Hukumomin tsaron Najeriya sun tabbatar cewa, dakarun tsaron hadin gwiwa na Afrika dake yaki da ayyukan ta'addanci a tafkin Chadi sun kashe mayakan Boko Haram 42.

Dakarun tsaron hadin gwiwar kasashen sun kaddamar da hare haren ne a ranar Juma'a wanda ya hada da ta kasa da ta ruwa a yankunan da mayakan Boko Haram suka mamaye, in ji Timothy Antigha, kakakin sojojin Najeriya, kana mai magana da yawun rundunar tsaron hadin gwiwar kasashen na Afrika.

An kaddamar da samamen ne a yankin Doron Naira, wani tsibiri dake tafkin Chadi, wanda ke kan iyakar garin Cross Kauwa na jamhuriyar Nijer da garin Baga na jihar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin Najeriya, in ji Antigha.

Dakarun tsaron hadin gwiwar sun hada da sojojin kasashen Najeriya, Chadi, Kamaru, Nijer da jamhuriyar Benin.

Soja guda ya mutu a lokacin arangamar da mayakan na Boko Haram, kana wasu sojojin 10 sun samu raunuka, in ji jami'in sojin.

A cewarsa, za'a ci gaba da kaddamar da hare hare kan mayakan, domin bude wuta da kuma murkushe babbar maboyar mayakan 'yan ta'addan dake tafkin Chadi.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China