Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Trump ya dakatar da lokacin dakile 'yan ci rani ba bisa doka ba
2019-06-24 10:43:05        cri

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana a kwanan baya cewa, an jima ana dage lokacin aikin dakile 'yan ci rani ba bisa doka ba har tsawon makonni biyu, da aka yi shirin gudanar da shi a jiya Lahadi, tare da baiwa jam'iyyar Republican da ta Democrat karin lokacin warware irin wannan matsala a siyasance.

A cewar Trump, idan bangarorin biyu ba su iya hada kansu don fitar da wani shiri daidaita matsalar 'yan ci rani a kan iyakar Amurka a bangare kudu ba, sai hukumar da abin ya shafa za ta tasa keyar wadannan 'yan cin rani ba bisa doka ba zuwa kasashensu asali.

An ba da labari cewa, hukuma mai kula da harkokin shiga kasar Amurka da kwastam karkashin ma'aikatar tsaron yankunan Amurka wato DHS a takaice, sun yi shirin gudanar da aikin dakile 'yan ci rani ba bisa doka ba daga ranar 23 ga wata a birane 10, abin da ya jawo hankulan jama'ar Amurka kwarai da gaske. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China