Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 11 sun mutu sakamakon harbe-harbe da aka yi a Virginia
2019-06-01 16:32:55        cri
Rundunar 'yan sandan birnin Virginia Beach na jihar Virginia dake gabashin Amurka, ta ce, an samu harbe-harbe mai tsanani a yammacin jiya Juma'a a birnin, wanda ya haddasa rasuwar mutane 11, tare kuma da raunata wasu 6.

Shugaban 'yan sandan birnin Jim Cervera, ya bayyana haka ne a jiya yayin wani taron manema labaru, inda ya kara da cewa, dan bindigar ma'aikaci ne na gwamnatin birnin, kuma ya riga ya mutu.

Kafin haka, wani labarin da rundunar 'yan sandan ta bayar a dandalin sada zumunta, ya ce lamarin ya faru ne a wani ginin dake cibiyar birnin. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China