Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An rantsar da shugaban Najeriya a zangon mulki na biyu
2019-05-30 09:20:27        cri

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya sha rantsuwar kama aiki a zango na biyu na shekaru hudu, gaban dandazon magoya bayan sa, yayin bikin rantsuwar da aka gudanar a filin wasa na Eagle Square dake birnin Abuja, fadar mulkin Najeriya.

Shugaba Buhari da mataimakin sa Yemi Osinbajo, sun yi rantsuwar ne bisa jagorancin mukaddashin babban mai shari'ar kasar Tanko Muhammad, kafin daga bisani a sassauto da tutar kasar, da ta tutar rundunar tsaro, aka kuma harba bindiga sau 21, a wani mataki na nuna muhimmancin bikin. Shugaban Najeriyar dai ya alkawartawa 'yan kasar aiwatar da manufofin ci gaba, da za su haifar da makoma mai haske a nan gaba.

Bayan shan rantsuwar, shugaba Buhari, ya kewaya don ganin faretin girmamawa da aka shirya masa. Ba dai wani shugaban wata kasar waje da ya halarci bikin rantsuwar. Ko da yake kafin zuwan ranar bikin, mahukuntan kasar sun ce za a takaita shagulgulan bikin rantsuwar ne domin rage kashe kudade.

A wani ci gaban kuma, gwamnatin Najeriyar ta ce ta gayyaci shugabannin kasashen duniya da dama, don halartar bikin ranar dimokaradiyyar kasar, wadda aka mayar ranar 12 ga watan Yuni.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China