Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya za ta rage haraji ga kamfanonin gina titinan mota a kasar
2019-05-29 10:05:28        cri

Gwamnatin Najeriya ta sanar a ranar Talata cewa, za ta bayar da rangwame ga masu zuba jari wadanda ke gudanar da ayyukan gina manyan titunan mota a fadin kasar.

Duk wani kamfanin dake gudanar da aikin gina titunan mota a kasar zai samu rangwame kudaden haraji kwantankwacin kudaden da ya zuba jari a ayyukan, kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya ambato ministar kudin kasar Zainab Ahmed tana bayyana aniyar gwamnatin.

"Gwamnatin Najeriya mai ci tana gudanar da ayyukan gina titunan mota masu yawa a kasar ta hanyar hadin gwiwa da al'umma," in ji ta. "Daya daga cikin tsarin da aka bullo da shi ya hada da shirin rage haraji ga masu aikin gina hanya, idan wani kamfani mai zaman kansa ya zuba jarinsa ya gina titunan mota, za su maido da kudaden da suka zuba jari ta hanyar kudaden harajin da za'a rage musu."

Gwamnati tana kokarin samar da hanyoyin rage kudaden haraji ko kuma kudaden fito, in ji ministar.

A baya bayan nan gwamnatin Najeriya ta bullo da wasu tsare tsare da nufin bunkasa hanyoyin samun karin kudaden shiga daga dukkan fannonin tattalin arzikin kasar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China