Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Takaddamar ciniki tsakanin Amurka da Sin na iya hargitsa tsarin tattalin arzikin duniya in ji wani jami'in Kenya
2019-06-18 19:39:03        cri
Babban sakataren jam'iyya mai mulki a kasar Kenya Raphael Tuju, ya ce takaddamar ciniki da Amurka ta tayar tsakanin ta da kasar Sin, na iya hargitsa tsarin hada hadar cinikayya, da ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya.

Tuju wanda ya bayyana hakan a ranar Litinin, ya ce cikin matakan da Amurka ta dauka, hadda dakatar da mu'amala da wasu kamfanonin fasaha na kasar Sin a sassan Amurka.

To sai dai kuma jami'in ya bayyana takardar bayanin da kasar Sin ta fitar domin bayyana matsayin ta kan wannan danbarwa, a matsayin wani muhimmin mataki na kyautata diflomasiyya, wanda kuma zai taimaka wajen kyautata shawarwari tsakanin sassan biyu.

Ya ce Kenya na goyon bayan cudanya tsakanin sassa daban daban, duba da cewa hakan ne makoma, kuma hanyar da tafi dacewa kasashen duniya su bi sau da kafa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China