Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya bukaci a kara azama wajen gina sabuwar makoma ga tsaron Asiya da cigaban shiyyar
2019-06-16 16:52:59        cri
A jiya Asabar shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci kasashen nahiyar Asiya da abokan huldarsu dasu hada kansu don gina kyakyyawar makoma ta fannin tsaro da cigaban Asiya karkashin sabon yanayin da ake ciki.

Da yake gabatar da jawabi a taron kolin matakan hadin kai da amincewar juna na Asiya karo na 5 wato (CICA), wanda aka gudanar da Tajikistan, Xi ya bukaci mambobin kasashen na CICA dasu rungumi manufar hadin gwiwa da juna da tabbatar dawwamamman tsaro, kuma su tabbatar da tsaro mai sigar shiyyar Asiya, domin cimma nasarar tabbatar da tsaron nahiyar ta Asiya bisa hadin gwiwa.

Da yake yabawa irin nasarorin da kasashen Asiya suka cimma wajen gina al'ummar Asiya mai kyakkyawar makoma a cikin 'yan shekarun da suka gabata, Xi ya karfafa gwiwar mambobin kasashen CICA da su nace kan manufofinsu, kuma su yi amfani da damar hadin gwiwa wajen tinkarar kalubaloli, kana su hada karfi-da-karfe wajen bude sabbin damammaki raya cigaban al'amurran tsaro da cigaban Asiya karkashin sabon yanayin da ake ciki.

Da yake karin haske game da irin rawar da kasar Sin ke takawa, shugaba Xi yayi alkawarin tsayawa tsayin daka wajen bin hanyar cigaba cikin lumana da kuma yin musayar damammakin cigaba daga dukkannin bangarorin da abin ya shafi, musamman ta hanyar hadin gwiwar shawarar ziri daya da hanya daya da kuma samar da yanayin kasuwa mafi inganci.

A ranar Juma'a, Xi ya isa wajen taron kolin CICA, kana da ziyarar aiki a kasar Tajikistan.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China