Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mai dakin shugaban Najeriya ta nuna damuwa game da yawan hare haren yan fashi a kasar
2019-06-03 10:39:06        cri

Matar shugaban kasar Najeriya Aisha Buhari, ta bayyana damuwa sakamakon yawaitar kashe kashen rayuka da 'yan fashi ke yi a kasar, inda ta bukaci hukumomin tsaron kasar da su hanzarta kawo karshen matsalolin tsaron dake addabar kasar.

Mai dakin shugaban kasar ta bayyana damuwarta ne a lokacin da take raba kayayyakin tallafi ga mutane sama da 25,000 wadanda harin 'yan fashi ya shafa a jahar Katsina dake shiyyar arewa maso yammacin kasar.

Ta ce ya zama tilas jami'an tsaron kasar su tashi tsaye kafin bata gari su hallaka al'ummar kasar.

Aisha Buhari ta ce wajibi ne al'ummar Najeriya su fito fili su bayyana abubuwa marasa dadi dake faruwa a kasar, domin zaburar da masu ruwa da tsaki wajen daukar matakan da suka dace.

A yan kwanakin nan, satar shanu ta kasance wani mummunan laifi dake cigaba da ta'azzara a Najeriya, inda al'amarin yafi Kamari a shiyyar arewacin kasar.

A halin da ake ciki, hukumomin tsaro a jahohin Sokoto, Katsina, Kaduna da Zamfara suna cigaba da yin aiki tare domin dakile ayyukan bata gari da suka addabar yankunan.

A watan Mayu, gwamnatin Najeriya ta haramta amfani da babura a makwabtan jahohin 7 da dazukan yankunan bisa dalilai na tsaro. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China