Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Huawei da AU sun kulla yarjejeniyar bunkasa fasahar sadarwa ta zamani
2019-06-02 14:37:18        cri

Fitaccen kamfanin fasahar nan na kasar Sin wato Huawei ya kulla wata yarjejeniyar fahimtar juna da kungiyar tarayya Afrika (AU) domin yin hadin gwiwar bunkasa fasahar sadarwa ta zamani wato (ICT).

An kulla yarjejeniyar tsakanin bangarorin biyu ne da nufin bunkasa hadin gwiwa kan fasahar sadarwa ta zamani, da abubuwan da suka shafi fasahar samar da bidiyon komai da ruwanka (IoT), da aikin kididdiga ta hanyar amfani da na'ura mai kwakwalwa, da fasahar 5G, da kuma fasahar kwaikwayon tunanin dan adama, kamfani na Huawei ne ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya fitar da yammacin ranar Juma'a.

Yarjejeniyar za ta kunshi gudanar da ayyukan fasahar zamani ta ICT da kuma yadda za'a taimakawa Afrika wajen bunkasa ci gaban fasahar zamani ta ICT a nahiyar, wanda zai shafi fannonin tsaron intanet, da kiwon lafiya ta hanyoyin ci gaban zamani, da ilmi da hanyoyin zamani da dai sauransu.

Dukkanin bangarorin biyu suna yin aiki tare da juna domin zakulo masu basira na cikin gida don ba su horo da nufin tinkarar kalubalolin ci gaban fasahar zamani a nan gaba a fannonin da suka shafi fasahohin zamani, in ji sanarwar.

Haka zalika yarjejeniyar za ta kara ba da damar samun damammaki na guraben aiki yi ga matasa ta hanyar samar musu da kwarewa a fannin ilmin fasahar sadarwa ta zamani.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China