Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin Huawei na kasar Sin zai zamanantar da biranen Afrika
2019-05-27 09:49:32        cri

Shahararren kamfanin sadarwar nan na kasar Sin Huawei ya sha alwashin mayar da biranen Afrika na zamani domin bunkasa yanayin ingantaccen muhalli, wani jami'i ne ya bayyana hakan.

Adam Lane, babban daraktan hulda da jama'a na kamfanin Huawei a kasar Kenya, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Nairobi cewa, biranen Afrika za su sauya zuwa na zamani ta hanyar amfani da sabbin fasahohin zamani a bangarorin da suka shafi samar da ruwa da makamashi, sadarwa, tsaro da inganta kiyaye rayuwar al'umma.

"A halin yanzu kamfanin Huawei ya fara tattaunawa da wasu biranen Afrika masu yawa domin samun nasarar zamanantar da biranen," Lane ya bayyana hakan ne a lokacin taron manyan shugabannin 'yan kasuwa gabanin gudanar da zagayen farko na babban taron MDD kan muhalli.

Tuni kamfanin na Huawei ya fara sanya fasahohinsa a wasu biranen kasashen Kenya, Najeriya da Botswana.

Lane ya ce, za'a iya amfani da sabbin fasahohin zamani wajen kula da albarkatun muhalli wanda hakan zai taimaka wajen kyautata yanayin biranen.

A cewar Huawei, ta hanyar amfani da mitoci irin na zamani wajen amfani da ruwa da lantarki, biranen Afrika za su iya rage hasarorin da ake samu da kuma inganta hanyoyin samun kudaden shigarsu.

Ya lura cewa, kasashen Afrika suna daga cikin biranen duniya dake saurin samun bunkasuwa.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China