Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kamfanin Huawei ya ce tushen matsalar cinikayyar Sin da Amurka shi ne matsayin ilimi
2019-05-22 16:28:09        cri

Shugaban kamfanin Huawei na kasar Sin Ren Zhengfei ya zanta da 'yan jaridun CMG a hedkwatar kamfaninsa dake birnin Shenzhen jiya Talata, inda ya bayyana cewa, ya kamata a kara maida hankali kan samar da ilimi daga tushe da koyar da ilimin sana'o'i, kuma tushen matsalar cinikayyar Sin da Amurka shi ne batun ilimi.

Ren ya ce, idan wata kasa na son zama mai karfi, dole a inganta muhimman ababen more rayuwar jama'a, abun da ya bukaci kyautata harkokin al'adu da samar da ilimi da inganta dabi'un dan Adam.

Ren ya kara da cewa, dole ne a yi kokarin samar da ingataccen ilimi ga yara manyan gobe, ta yadda za su bada gudummawarsu ga gina kasa a nan gaba.

Har wa yau, Ren ya ce, tushen matsalar cinikayyar Sin da Amurka a halin yanzu shi ne batun ilimi, yana mai cewa kasa ba za ta samu makoma mai haske ba, idan ba ta bude kofa ga kasashen waje ba. A cewarsa, bude kofa ga kasashen waje na bukatar lafiya mai inganci, kuma lafiya mai inganci na bukatar ilimi.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China