Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-09 20:56:11    
Kungiyar wasannin fasaha ta nakasassu ta kasar Sin ta burge jama'a

cri

A gun bikin, Mr.Yang Haitao, mawaki makaho, wanda ya rera wata waka mai taken "gidan gaskiya" cikin Sinanci da kuma Turanci, da Mr.Jin Yuanhui, wani makaho mai kada piano, wanda ya kada kide-kiden da Chopin ya tsara, dukansu sun zo ne daga kungiyar wasannin fasaha ta nakasassu ta kasar Sin.

An dai kafa kungiyar wasannin fasaha ta nakasassu ta kasar Sin ne a shekarun 1980, kuma yanzu yawan 'yan kungiyar ya kai sama da 150, wadanda su kan kai ziyara zuwa kasashe daban daban, don nuna wa 'yan kallo na kasashen waje wasanni.

Lokacin da ya tabo magana a kan bikin fara wasannin Olympic na nakasassu, Mr.Jin Yuanhui ya yi farin ciki sosai ya ce, "Na nuna abin da nake ji zuciyata, wato godiya da ba a iya bayyana ta magana ba, ga dukan 'yan kallo da ke gaban telebijin da kuma a wajen bikin, da kuma duk wadanda suka nuna mini kulawa da goyon baya."

kungiyar wasannin fasaha ta nakasassu ta kasar Sin ta kasance tamkar wani babban iyali, inda 'ya'yanta ke kulawa da juna da kuma zaman jituwa da juna. A lokacin wasannin Olympic da kuma wasannin Olympic na nakasassu, suna shirin gabatar da wasanni sama da 40 ga 'yan wasa da kuma abokai na gida da na waje. Da alamun hannu ne shugabar kungiyar, malama Tai Lihua, ta ce, suna so ta hanyar nuna wasannin fasaha na musamman, su bayyana ra'ayoyin nakasassu da kuma fatan alheri na yara nakasassu ga wasannin Olympic guda biyu.


1 2 3