Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-09 20:56:11    
Kungiyar wasannin fasaha ta nakasassu ta kasar Sin ta burge jama'a

cri

A gun bikin rufe wasannin Olympic na nakasassu na Athens da aka yi yau da shekaru hudu da suka wuce, wasan fasaha mai suna "gunki mai hannuwa da yawa" da kungiyar wasannin fasaha ta nakasassu ta kasar Sin ta nuna ya burge dimbin jama'a, sabo da haka, kungiyar ta sami alaka ta musamman da wasannin Olympic na nakasassu. A gun bikin fara wasannin Olympic na nakasassu na Beijing da aka yi kwanan baya ba da jimawa ba, 'yan kungiyar sun sake burge jama'a da wasannin da suka nuna.

Malama Mao Yujia, wata mazauniyar birnin Beijing ta ce, rawar da kurame 109 suka yi tare da wata yarinya mai suna Li Yue, wadda ta tsira da ranta daga girgizar kasa mai tsanani da ta auku a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan na kasar Sin, ta sosa mata rai sosai. "An sosa mana rai sosai, musamman ma lokacin da su mutane da yawa suka yi rawa tare bisa alamun hannu da malamamsu suka nuna, tamkar na sake ganin 'gunki mai hannuwa da yawa", har ya fi burge ni, na ji mutum na da matukar karfi."


1 2 3