Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-03 15:23:06    
Jihar Ningxia tana dukufa kan shawo kan kwararowar hamada domin raya al'umma mai jituwa

cri

Kwararowar hamada mai tsanani ta kawo cikas sosai ga bunkasuwar tattalin arziki na gundumar Yanchi, haka kuma wannan shi ne dalili mafi muhimmanci da ya sanya fararen hula na wurin su fama da talauci. Domin kyautata wannan mumunan halin da ake ciki kwata kwata, gwamnatin gundumar ta gabatar da wani ra'ayi, wato fama da kwararowar hamada domin samun bunkasuwa. Liu Weize, mataimakin shugaban hukumar kula da bishiyoyi ta gundumar Yanchi ya gaya mini cewa,

"kwararowar hamada ta yi illa sosai ga dan Adam, musamman ma ga yanayin ayyukan gona da zaman manoma na wurin. Muddin ta hanyar fama da kwararowar hamada, da kuma kyautata karfin gonaki wajen samar da amfanin gona, sai za a iya kyautata ingancin zaman rayuwar manoma."

Sabo da haka gwamnatin gundumar Yanchi ta dauki matakai a jere wajen dasa bishiyoyin da ke dace da halin da gundumar ke ciki. Kuma bisa kokarin da aka yi a shekaru da yawa da suka gabata, an samu babban ci gaba wajen fama da kwararowar hamada.

Ban da yaki da hamada ta hanyar kimiyya, gwamnatin gundumar Yanchi tana dora muhimmanci kan hadin gwiwa tare da kasa da kasa, kuma daya bayan daya ne ta samun kudaden kyauta da kasashen Japan da Jamus suka samar wajen dasa biushiyoyi. Liu Weize, mataimakin shugaban hukumar kula da bishiyoyi ta gundumar Yanchi ya bayyana cewa,

"muhimmin halittu na gundumarmu ya samu kyautatuwa sosai bisa taimakon da kasashen waje suka bayar. Ba kawai kasashen waje sun samar da kudade gare mu ba, har ma sun ba mu fasahohi da sakamako mai kyau wajen fama da kwararowawr hamada. Sabo da haka muna da imani sosai wajen gudanar da wannan aiki."


1 2 3