Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-03 15:23:06    
Jihar Ningxia tana dukufa kan shawo kan kwararowar hamada domin raya al'umma mai jituwa

cri

Jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kai ta kasar Sin tana daya daga cikin jihohin da ke fama da hamada mai tsakani a duk fadin kasar. A cikin shekaru da yawa da suka gabata, har kullum jihar Ningxia tana kudufa kan aikin shawo kan kwararowar hamada da kuma yaki da ta, kuma ta kama gaba wajen tabbatar da samun janyewar hamada a kasar Sin. To, yanzu zan gabatar muku wani bayani kan yadda jihar Ningxia ke fama da kwarowar hamada.

Gundumar Yanchi tana gabashin jihar Ningxia, kuma tana bakin hamadar Mu Us. Sabo da illar da halittu da dan Adam suka yi a da, kwararowar hamada a gundumar tana ta tsananta. Kamar yadda mazaunan wurin su kan ce, ko a lokacin baraza, ko a lokacin hunturu, idan an yi iska, to za a samu rairayi a ko ina, haka kuma tudun rairayi ya fi dakuna tsayi. Lokacin da aka tabo mumunan muhallin halittu na wancan lokaci, Yu Hu, wani dan kauyen Yu Zhuangzi na gundumar Yanchi ya bayyana cewa,

"a lokacin da, idan iska ta buga, har ma ba a iya ganin wuraren da ke da nesa mita 10 ba, tumaki sun bace, mutane ba su iya koma gidaje ba. Har ma wasu yara sun mutu sakamakon benne a cikin hamada."


1 2 3