Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-12 15:56:21    
Fahimtar addinin Buddha a manyan duwatsun Emeishan da Leshan

cri

In masu yawon shakatawa suna son su kara fahimtar addinin Buddha, to, ziyarar mutum-mutumin na babban Buddha na 'Leshan' yana iya biyan bukatunsu. Bayan ganin wannan mutum-mutumin Buddha mafi girma a duk duniya, tabbas ne za su ji mamaki da imanin da masu bin addinin Buddha suka nuna ga addinin Buddha a zamanin da.

An sassaka wannan mutum-mutumi mai tsayin mita 70 ko fi a jikin babban dutse don yin kaka-gida a koguna. Tsayinsa ya yi daidai da na wannan babban dutse. An yi shekaru misalin 90 ana sassaka shi. Mutanen yanzu sun ji mamaki sosai domin nagartacciyar fasaha ta zamanin da, da kuma jaruntakar da mutane suka nuna a lokacin da suka sassaka wannan mutum-mutumin Buddha.

Jama'a masu sauraro, kyawawan wurare masu ni'ima na manyan duwatsun Emeishan da Leshan da kuma al'adun addinin Buddha mai dogon tarihi da ban mamaki sun cancanci mutane da su kai musu ziyara.

To, kafin mu sa aya ga shirinmu na yau, bari mu maimaita tambayoyin da muka yi muku. Da farko ko babban dutse na Emeishan na daya daga cikin wurare masu tsarki na addinin Buddha na kasar Sin ko a'a? Na biyu, mutum-mutumin babban Buddha na Leshan mutum-mutumi ne mafi girma na Buddha a duk duniya, tsayinsa ya kai mita nawa ne?(Tasallah)


1  2  3