Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-12 15:56:21    
Fahimtar addinin Buddha a manyan duwatsun Emeishan da Leshan

cri

Ganiyar babban dutse na Emeishan da ake kiransa 'kololuwa ta zinariya', wato Golden Summit a Turance, anihin wannan babban dutse ne. Ban da manyan dakuna masu girma guda 3, mutum-mutumin Bodhisattva mai suna Puxian mai tsayin mita misalin 48 da aka yi da zinariya ya fi jawo hankulan mutane.

Malam Li Genyuan wanda ke nuna imani sosai ga addinin Buddha, ya zo babban dutsen Emeishan daga kasar Korea ta Kudu don bauta wa Bodhisattva mai suna Puxian. Ya ce,

'Na ga mutum-mutumin Bodhisattva mai suna Puxian mai girma haka a babban dutse na Emeishan a wannan gami, na ji a zuciyata cewa, kasar Sin wata kasa ce mai girma. Na durkusa a gaban mutum-mutumin Bodhisattva mai suna Puxian sau 10, na durkusa sau 3 a cikin manyan dakunan 3, ban da wannan kuma, na ba da kyautar kudi, ko da yake ba ya da yawa, amma ina son in bayyana imanina.'

Kololuwar zinariya ta babban dutse na Emeishan ba ma wurin aikin hajji ne kawai ba, har ma wuri ne mafi dacewa da jin dadin kallon fitowar rana da kuma tekun gajimare. Bugu da kari kuma, in an taki sa'a, masu yawon shakatawa za su iya ganin hasken Buddha mai matukar daraja a wannan ganiyar babban dutsen. Ana kiran wannan haske Buddha's Halo a Turance. An samu wannan haske mai ban mamaki ne saboda hasken rana da tsare-tsaren kasa da sauran dalilai sun taka rawarsu tare.

Addinin Buddha ya taka muhimmiyar rawa a fannin bunkasuwar babban dutsen Emeishan, ya kyautata al'adu na wannan babban dutse. Muhimmancin gidajen ibada na addinin Buddha da mutum-mutumin Buddha ya yi daidai da na ni'imtattun wurare na babban dutse na Emeishan. Shi ya sa, Hukumar ilmi da kimiyya da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya ta tanadi wannan babban dutse a cikin takardar sunayen wuraren tarihi na al'adu da na halitta na duniya.


1  2  3