
A farkon watan Afrilu , kungiyar wakilan wasan kwallon tebur ta kasar Amurka ta sake kawo ziyara a nan birnin Beijing. A lokacin ziyararsu ba kawai sun yi gaisuwa da tsofafin 'yan wasan kwallon Pingpong na kasar Sin ba , har ma sun sake dauki kulkin wasa sun yi gasa da takwaransu na kasar Sin . Bugu da kari kuma za su kai ziyara a Dakuna da filayen wasannin Olympic na yanayin zafi na 29 da na wasannin Olympic na gajiyayyu . Gwamnatin birnin Beijing da Kwamitin shirya wasan Olympic na Beijing suna mai da muhimmanci sosai kan aikin shirya wasan gajiyayyu . A cikin shekarar da ta shige , an yi wasu aikace-aikace cikin tsanaki kuma za a dauki matakai masu yawa a cikin sabuwar shekara don kai aikin hidima mai kyau ga 'yan wasa gajiyayyu da masu yawon shakatawa .
A lokacin gasar cin kwaf na kwallon tebur ta karo na 31 na duniya da aka yi a shekarar 1971 a birnin Nagoya na Japan, Zhuang Zedong Shahararren 'dan wasan kwallon Pingpong na kasar Sin ya ba da kyauta ga Glenn Cowan , 'dan wasa na kasar Amurka . Mr. Cowan shi ma ya mayar da kyauta daban ga Mr. Zhuang . Wannan batu ya jawo hankulan mutane kwarai da gaske .A wannan shekara bangaren Sin ya gayyaci kungiyar wakilan kasar Amurka da ta kawo ziyara a nan kasar Sin . Su ne sun zama Amerikawa na karo na farko da suka shika cikin kasar Sin . Wannan al'amari ya zama abin share fage na kasashen waje Sin da Amurka suka kulla huldar diplomasiya . A shekarar 1972 , Richard Nixon , shugaban kasar Amurka ya kawo ziyarar aiki a kasar Sin.(Ado ) 1 2 3
|