
Wakilin Rediyon kasar Sin ya ruwaito mana labari cewa , kwallon tebur kwallo ne na kasar Sin . Ya kawo wa kasar Sin lambobin zinarya na duniya masu yawan gaske . Amma duk da haka ba kawai wannan karamin kwallo ya ba da taimako a wajen wasannin motsa jiki ba , har ma ya ba da babban taimako a wajen harkokin waje . A cikin shekaru fiye da 30 da suka shige , da farko dai diplomasiyar kwallon tebur ta ingiza yalwatuwar huldar tsakanin kasar Sin da kasar Japan , sa'an nan kuma ya rushe kankarar kan hulda tsakanin kasar Sin da kasar Amurka .
A ran 3 ga wata nan a nan birnin Beijing , Tang Jiaxuan, wakilin harkokin kasar Sin ya gana da 'yan Kungiyar wakilan kasar Japan wadda Koji Kimura , wakilin musamman na Kungiyar wasan kwallon tebur ta Japan ya ke jagoranci . Kungiyar ta kawo ziyara ne don tuna da cikon shekaru 50 na musaye-musayen wasannin motsajiki tsakanin Japan da Sin.
1 2 3
|