Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Sin ta tallafawa asibitin kasar Ghana da kayayyakin kiwon lafiya
2020-11-11 11:42:31        cri
Gwamnatin kasar Sin ta bayar da gudunmawar kayayyyakin kiwon lafiya ga asibitin kawancen Sin da Ghana a ranar Talata.

Babban jagoran tawagar jami'an lafiyar kasar Sin dake Ghana, Shi Yongyong ya ce, tun lokacin da suka ziyarci asibitin suke samar musu da ingantattun kayayyakin kiwon lafiya. Sakamakon yadda suka lura da cewa asibitin yana fama da karancin kayayyakin kiwon lafiya. Ya ce sun yi bakin kokarinsu wajen tallafa musu, kuma gwamnatin kasar Sin ce ta samar da kayayyakin kiwon lafiyar ga asibitin.

Anastasia Yirenkyi, wani jami'i a ma'aikatar lafiyar kasar Ghanan wanda ya karbi gudummawar a madadin ministan lafiyar kasar, ya ce, "Da abokin daka akan sha gari. Lallai kun taimaka mana, kuma kuna cigaba da taimaka mana."(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China