Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Najeriya sun kashe 'yan Boko Haram 5 tare da kubutar da mutane hudu
2020-11-11 10:52:43        cri
Kimanin mayakan Boko Haram biyar ne aka kashe kana an kubutar da wasu mutane hudu da aka yi garkuwa da su yayin wani samamen da dakarun sojojin Najeriya suka kaddamar a shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Kakakin rundunar sojojin Najeriya Benard Onyeuko, ya ce, an kashe mayakan na Boko Haram ne a ranar Litinin a musayar wutar da suka yi da mayakan a kauyen Buni Gari, dake karamar hukumar Gujba a jahar Yobe dake shiyyar arewa maso gabashin kasar, ya tabbatar da hakan.

Onyeuko ya ce, akwai kuma wasu mayakan 'yan ta'addan masu yawa da suka samu raunukan harbin bindiga a lokacin musayar wutar, a lokacin da suka yi yunkurin shiga kauyen na Buni Gari inda yunkurin nasu ya ci tura.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China