Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AEC: Ya zama wajibi kasashen Afirka su dauki matakan daidaita yanayin da ake ciki a fannin raya makamashi
2020-11-11 10:13:27        cri
Cibiyar raya makamashi ta Afirka ko AEC a takaice, ta ce duba da yadda cutar COVID-19 ta yi mummunan tasiri ga Afirka, kamata ya yi gwamnatoci da masu samar da makamashi na nahiyar, su dauki matakan ci gaba da gogayya da sauran takwarorin su.

Ofishin AECn ya bayyana hakan ne a jiya Talata, yayin fitar da rahoton sa na hasashen yanayin makamashi na Afirka a shekarar 2021 dake tafe. Da yake tsokaci game da hakan, babban mataimakin shugaban cibiyar Mr. Verner Ayukegba, ya ce rahoton ya kunshi fashin baki game da kalubale, da hasashen makoma, da kuma shawarwarin warware matsalolin da fannin ke fuskanta.

Mr. Ayukegba ya yi kira da a kawar da manufofi masu haifar da rashin tabbas a fannin, da kuma gaggauta aiwatar da ayyuka. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China