Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
FOCAC tana kawo wa kasashen Afirka alheri na a-zo-a-gani
2020-11-10 14:23:23        cri

Kwanan baya, babban edita na jaridar Leadership ta kasar Nijeriya Bukola Ogunsina, ya wallafa wani sharhi mai lakabin "cikar shekaru 20 da kafuwar FOCAC, da huldar da ke tsakanin Nijeriya da Sin" a jaridar, inda ya ce taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin kasashen Sin da Afirka, wani muhimmin dandali ne na yin hadin gwiwar a-zo-a-gani a tsakanin bangarorin 2. Ya ce an samu sakamako da dama cikin shekaru 20 da kafuwar dandalin, kana kasashen Afirka sun ci gajiyar dandalin.

Karkashin dandalin na FOCAC, an daga huldar da ke tsakanin kasashen Afirka da Sin zuwa huldar abokantaka da hadin gwiwa daga dukkan fannoni bisa manyan tsare-tsare. Ya zuwa shekarar 2019, jimilar jarin da kasar Sin ta zuba a kasashen Afirka kai tsaye ta kai dalar Amurka biliyan 49.1 baki daya, wadda ta karu kusan sau 100 bisa ta shekarar 2000. Sa'an nan kuma, jimilar kudaden ciniki a tsakanin Sin da Afirka ta kai dalar Amurka biliyan 208.7, wanda ya karu da sau 20 bisa na shekarar 2000. A shakaru 11 a jere ne kasar Sin ta kasance abokiyar ciniki mafi girma ta Afirka.

Shekarar 2021 mai zuwa, shekara ce ta cika shekaru 50 da kulla huldar jakadanci a tsakanin Nijeriya a Sin. Don haka a cewar Bukola Ogunsina, kamata ya yi Nijeriya ta yi amfani da wannan dama, wajen gaggauta aiwatar da sakamakon da aka samu a yayin taron koli na Beijing, da habaka hadin gwiwar cin moriyar juna a tsakanin kasashen 2, a kokarin ciyar da huldar da ke tsakaninsu gaba. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China