Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanan Afirka sun bayyana bukatar bunkasa makamashi daga tururin karkashin kasa
2020-11-10 11:14:10        cri
Sama da kwararru da wakilan gwamnatocin Afirka 500 ne suka halarci taron mako guda, game da yayata bukatar bunkasa makamashi da ake iya samarwa daga tururin karkashin kasa.

Yayin taron da ya gudana a birnin Nairobin kasar Kenya, kwararru a fannin sun fitar da wata sanarwa, wadda ta bayyana bukatar yayata albarkatun makamashi daga tururin karkashin kasa a matakai na ilimi da tsara manufofi, ta yadda za a kai ga tsara dabaru da ka'idojin aiki a fannin.

Kwararrun sun kuma bayyana aniyar su, ta yin hadin gwiwa da sauran masu ruwa da tsaki, karkashin lemar sabuwar cibiyar Afirka da aka kafa domin binciken makamashi daga tururin karkashin kasa, wajen bunkasa cin gajiya daga wannan fanni.

Kwararrun da suka hada da ministocin makamashi na kasashe mahalarta taron, sun kuma amince da bukatar kara hada kai, musamman a bangaren samar da kwarewa ga masu rajin inganta wannan fasaha, ta yadda za a kai ga cimma gajiya da bunkasa bangaren.

Da yake tsokaci game da hakan, darakta, kuma wakiliyar ofishin hukumar MDD mai lura da muhalli a Afirka ko UNEP, Juliette Biao Koudenoukpo, ta ce sakamakon taron zai ingiza nasarar kuduri na 7, cikin kudurorin wanzar da ci gaba na MDD SDGs, wato kudurin samar da makamashi mai tsafta a duniya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China