Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An sake komawa zaman taron hukumar WHO
2020-11-10 11:13:30        cri
A jiya 9 ga wata ne aka sake komawa zama na 73, na hukumar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta kafar intanet, a birnin Geneva na kasar Switzerland.

A jawabin da ya gabatar a gun bikin bude zaman, babban darektan hukumar, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewa, gano bakin zaren warware matsalar COVID-19 a kimiyyance, tare kuma da hadin gwiwa da juna, shi ne hanya daya tilo da za a iya bi wajen shawo kan annobar a fadin duniya.

Ban da haka, taron da aka yi a wannan rana, ya kuma ki amincewa da saka shawarar da wasu kasashe kalilan suka gabatar, ta "gayyatar yankin Taiwan ya halarci taron hukumar a matsayin mai sa ido cikin abubuwan da za a tattauna a gun taron".

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China