Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan kwallon kafar Ghana 3 sun harbu da COVID-19 gabanin fara buga wasannin kakar bana
2020-11-09 13:53:35        cri
'Yan kungiyar kwallon kafa ta "Accra Hearts of Oak" dake kasar Ghana su 3 sun harbu da cutar COVID-19, gabanin fara buga gasar zakarun kwallon kafar kungiyoyin kasar. A cewar mahukuntan kungiyar, duk da ba a sanar da sunayen 'yan wasan ba, tuni aka gabatar da su ga fannin kiwon lafiya domin killace su.

Tun daga watan da ya gabata ne dai hukumar kwallon kafar kasar Ghana ko GFA, ta fara aiki tare da kwamitin kar ta kwana da gwamnatin kasar ta kafa, domin yiwa daukacin 'yan wasa, da masu horas da su, da jami'ai na kungiyoyi 18 dake buga gasar zakarun kulaflikan kasar gwajin cutar ta COVID-19.

Babu tabbas game da ko 'yan wasan da suka harbu da cutar za su warke, kafin fara buga kakar wasannin ta 2020 zuwa 2021, wadda aka tsara farawa a ranar 14 ga watan nan na Nuwamba. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China