Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bude bikin baje kolin cinikayyar kayayyakin al'adu da yawon bude ido a Yiwu
2020-11-09 12:14:59        cri
An bude bikin baje kolin kayayyakin al'adu da na yawon bude ido, jiya Lahadi a birnin Yiwu, karamar kasuwa mafi tagomashi a duniya dake lardin Zhejiang na gabashin kasar Sin.

Ma'aikatar al'adu da yawon bude ido ta kasar Sin ce ta shirya baje kolin da hadin gwiwar majalisar inganta cinikayya da kasashen ketare ta kasar da gwamnatin jama'ar lardin Zhejiang.

Bikin ya gabatar da wasu sabbin nau'o'in fasahohi da harkokin kasuwanci, kamar manyan bayanai da na'urar AI da sauransu.

Bikin na bana zai kare ne a gobe, 10 ga wata. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China