Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bikin CIIE da ake gudanarwa a Sin ya nuna kuzarin kirkire-kirkiren kasar
2020-11-06 18:50:11        cri

A halin yanzu ana gudanar da bikin CIIE, wato baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin daga ketare karo na uku a birnin Shanghai dake kudancin kasar, tunanin kirkire-kirkire ya sake jawo hankalin al'ummun kasa da kasa.

A karo na farko, an fitar da sabbin kayayyaki, da sabbin fasahohi, da sabbin hidimomi a yayin bikin. Alal misali kamfanin ABB yana nunawa 'yan kallo sabuwar na'urarsa, wato na'urar tantance fitowar iskar gas da aka adana a cikin jikin jirgin sama maras matuki, na'urar tana amfani da fasahar kamfanin ABB, da tsarin taurarin dan Adam masu shawagi na Beidou na kasar Sin, wadda ke taka rawa wajen tabbatar da tsaron amfanin iskar gas.

Hakika a cikin cibiyar nune-nunen bikin CIIE, kayayyakin da ake nunawa wadanda suka hada da fasahohin zamani na kasa da kasa suna da yawan gaske, lamarin da ya nuna cewa, muddin an bude kofa ga ketare, an kuma gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, za a iya ciyar da kimiyya da fasaha gaba yadda ya kamata.

Ko shakka babu, dalilin da ya sa bikin ya jawo hankalin 'yan kasuwar kasa da kasa shi ne babbar kasuwa da kasar Sin ke da ita, inda ake kokarin tabbatar da ci gaban kasar cikin inganci, a don haka ya dace a gwada sabbin fasahohi, da sabbin kayayyaki na kasar ta Sin.

Wasu kamfanonin ketare wadanda ke gudanar da harkokinsu a kasar Sin a cikin 'yan shekarun da suka gabata, suna sa ran za su fara aikinsu daga kasuwar kasar Sin domin shiga kasuwar duniya, kamar yadda shugaban kamfanin L'OREAL reshensa dake kasar Sin Fabrice Megarbane ya bayyana. Mr. Mgarbane ya ce halartar bikin CIIE na kasar Sin zai kawo hidimomin kayayyaki na gari, da shirin daidaita matsaloli zuwa ga kasar Sin daga ketare, haka kuma zai yada sakamakon kirkire-kirkiren kasar Sin zuwa ga ketare, duk wadannan za su amfani masu sayayya a fadin duniya.

A cikin shawarwarin da aka gabatar yayin da ake tsara shirin raya kasa bisa shekaru biyar biyar karo na 14 a kasar Sin, gwamnatin kasar ta mai da hankali matuka kan kirkire-kirkire, kuma a gun bikin kaddamar da baje kolin na CIIE a kwanan baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping shi ma ya bayyana cewa, kasarsa za ta ci gaba da kara habaka bude kofarta ga ketare, domin ingiza cinikayyar waje ta hanyar kirkire-kirkire. Ya ce tabbas wannan kudurin zai taimaka wajen cudanyar fasahohi tsakanin kasa da kasa.

Hakika an lura cewa, kasar Sin ta riga ta shiga sabon matakin samun ci gaba, kuma babbar kasuwarta za ta kara jawo hankalin 'yan kasuwar kasa da kasa, saboda suna ganin cewa, kasar Sin dake yin kirkire-kirkire tana da makoma mai haske.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China