Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ana sa ran kasuwar Sin za ta kasance kasuwa ta duniya
2020-11-05 19:02:18        cri

A bikin kaddamar da baje kolin CIIE, wato bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na uku da aka kaddamar a jiya Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da wani muhimmin rahoto ta kafar bidiyo, inda ya bayyana cewa, yana fatan kasuwar kasar Sin za ta kasance kasuwa ta duniya, kuma kasuwar samun riba tare, kana kasuwar al'ummun kasa da kasa. Wannan tsokaci na sa ya nuna fatan kasar Sin na raba damammakin ci gaba a kasuwar kasar da sauran kasashen duniya, tare kuma da ingiza farfadowar tattalin arzikin duniya.

Shugaban kamfanin Qualcomm na Amurka reshen kasar Sin Meng Pu, ya bayyana yayin da yake zantawa da wakilinmu cewa, matakan da kasar Sin za ta dauka domin nuna goyon baya ga kamfanonin ketare, ta dandalin CIIE da sauransu, za su taimaka wa hadin gwiwar dake tsakanin kamfanonin kasar Sin da na ketare.

A bangaren bude kofa ga ketare, da gudanar da hadin gwiwar dake tsakaninta da sauran kasashe, ba ma kawai kasar Sin ta yi la'akari sosai ba, har ma ta dauki matakai a kan lokaci. A halin da ake ciki yanzu, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira ga kasashen duniya, da su sanya kokari tare, domin gudanar da hadin gwiwar dake tsakaninsu tare kuma da samun moriya tare, yunkurin da ya samar da manufar da ta dace, yayin da ake gudanar da harkokin kasa da kasa, inda ya jaddada cewa, ya kamata manyan kasashen duniya su yi jagoranci bisa misali, kana kasashe masu karfin tattalin arziki su rika aiwatar da matakai bisa dacewa, kana kasashe masu tasowa su taka rawar gani, wajen yayata bude kofa da aiki tare bisa tsari, kamata ya yi a mayar da tsokacin sabon tunanin dakile rikicin duniya da ingiza ci gaba a duniya.

Yayin bikin CIIE, shugaba Xi ya bayyana sabbin matakai da kasarsa za ta aiwatar a fannin bude kofa daga dukkanin fannoni, wato kasarsa za ta bullo da jerin hajojin da za a dakatar, a fannin cinikayyar hidimomi na kasa da kasa, za ta kuma fadada wasu sassan, kamar na raya tattalin arziki ta amfani da fasahohin zamani na yanar gizo, da zurfafa sauye sauye, da kirkire kirkire a fannin cinikayya da zuba jari, da sakarwa kasuwa mara, da samar da kyakkyawan yanayi. Kuma Sin za ta rage jerin fasahohin da aka hana, ko aka takaita shigo da su, ta yadda hakan zai ba da damar samar da kyakkyawan yanayi na musayar fasahohin zamani tsakanin kasa da kasa. Kana Sin za ta ci gaba da inganta tsarin shari'ar ta, ta yadda zai dace da na kasa da kasa ta fuskar kara bude kofa, da yin komai a bude, da karfafa kariya ga ikon mallakar fasaha, da ma yadda za su samar da kariyar shari'a, da moriyar masu zuba jari na kasashen waje, duk wadannan sun nuna anniyar kasar Sin, ta gina kasuwarta har ta kasance kasuwa ta duniya.

Bisa hasashen da shugaba Xi ya yi, an ce, a cikin shekaru goma masu zuwa, gaba daya adadin kayayyakin da za a shigo da su kasar Sin zai kai darajar dala triliyan 22, lamarin ya nuna cewa, babbar kasuwar kasar Sin za ta kawo babbar moriya ga duk duniya, wanda hakan zai sake shaida cewa, kasar Sin tana ci gaba da yin matukar kokari, domin gina kyakkyawar makomar bil Adama.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China