Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dorewar dangantakar Sin da Afrika bayan annobar COVID-19
2020-11-05 11:21:12        cri


Tun a farkon wannan shekarar ne duniya ta tsinci kanta a cikin mawuyacin hali sakamakon barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19, koda yake, za a iya cewa, duk da halin da ake ciki na yaki da annobar a sassan duniya, dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika tana cigaba da karfafuwa yayin da bangarorin biyu ke cigaba da yin hadin gwiwa game da shirye shirye daban daban na yaki da annobar.

A kwanakin baya ne cibiyar nazarin al'amurran tsaron alumma ta Gusau Institute dake Najeriya, tare da hadin gwiwar cibiyar nazarin al'amurran Afrika dake jami'ar Zhejiang Normal University, wato ZJNU, dake kasar Sin, suka shirya taron dandalin muyasar ra'ayoyi na Abuja Forum 2020, a tsakanin kwararrun masanan kasashen Afrika da na kasar Sin ta kafar intanet mai taken "Dorewar dangantakar Sin da Afrika bayan annobar COVID-19".

Manufofin shirya taron su ne, gabatar da sabon nazari game da dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika ta hanyar gayyato masana wadanda ke da kwarewa game da alakar dake tsakanin Sin da Afrika, da kuma masu fashin baki kan dangantakar tattalin arziki a tsakanin Sin da Afrika, da batun dangantakar kasuwanci tsakanin Sin da Afrika, da dangantaka tsakanin mutum da mutum da sauran batutuwa dake shafar dangantakar al'adu tsakanin Sin da Afrika. Batu na biyu shi ne, bunkasa tattaunawa a tsakanin bangarorin Sin da Afrika, da kuma kara yin hadin gwiwa daga dukkan fannoni tsakanin bangarorin biyu.

Taron ya samu halartar masana, da kwararru a fannoni daban daban na Afrika da Sin.

Raila Amolo Odinga, wani fitaccen dan siyasar kasar Kenya ne, wanda ya taba rike mukamin firaministan Kenya daga shekarar 2008 zuwa 2013, kana ya rike mukamai a matakai daban daban a kasar ta Kenya, ya gabatar da jawabinsa inda yayi tsokaci game da tarihin dadaddiyar dangantakar dake tsakanin Afrika da kasar Sin inda ya tabo kadan daga cikin tarihin hadin gwiwar bangarorin biyu.

Yace, "Ina matukar murna da farin cikin halartar wannan tattaunawar game da hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afrika, Sin da Afrika suna da dadadden tarihin hadin gwiwa a tsakaninsu wanda ba zai yiwuwa a iya bayyanawa a cikin gajeren lokaci ba saboda tun a karni na takwas akwai dangantaka a tsakanin bangarorin biyu, a wajejen karni na tara Sin ta gano wasu kasashen Afrika da dama a yankunan gabashin Afrika kamar kasashen Kenya, tsibirin Zanzibar, da Somaliya, a lokacin daular Ming wasu jiragen ruwan Sin kusan 300 da suka yada zango a tekun Indiya sun sauka a yankin gabar tekun gabashin Afrika. Nasarar da juyin juya halin da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta samu a shekarun 1949 yayi sanadiyyar wasu Sinawa masu yawa sun yi hijira zuwa yankunan Afrika kuma ya zuwa shekarun 1950s an kiyasta akwai Sinawa kusan dubu 300 dake rayuwa a kasashen Mauritius, Madagaska, da Afrika ta kudu. Gwamnatin jamhuriyar jama'ar kasar Sin ta taka gagarumar rawa wajen fafutukar neman 'yancin kasashe daga hannun turawan mulkin mallaka kuma ta bayar da babbar gudunwama wajen samun 'yancin kan kasashen nahiyar Afrika. Marigayi Zhou Enlai, wanda a wancan lokacin shine firaministan kasar Sin, a game da Afrika, a wancan lokacin a shekarun 1963 zuwa 64, wancan lokacin shine mafarin kulla huldar diflomasiyya a tsakanin Sin da Afrika, matakin da ya biyo bayan tura tawagar jami'an kiwon lafiya Sinawa masu yawan gaske zuwa kasashen Afrika, da zuba jari a fannanin samar da kayayyakin more rayuwa. Daya daga cikin muhimman ginshikin cigaba shine, gina layin dogo na Tazam ko Tazara wanda ya kai nisan kilomita 1860 wanda aka kammala aiki ginawa a shekarar 1976 wanda ya hade tashar ruwan Darassalam zuwa wasu bangarorin kasar Zambiya, hakika, wani babban al'amari mai muhimmanci shine, dagantakar dake tsakanin Sin da Afrika daga shekarar 1981 zuwa 2015, kasar Sin tayi nasarar fitar da alummar Sinawa sama da miliyan 850 daga kangin talauci. Cikin wa'adin shekaru 35 kazal, haka zalika, a shekarar 2015 kasar Sin ta kaddamar da wani shirin fitar da mutane miliyan daya daga kangin talauci cikin kowane wata, Afrika, karkashin ajandar kungiyar tarayyar Afrika AU mai rajin samar da dawwamamman cigaban nahiyar nan da shekarar 2063, ta daura aniyar samar da kyakkyawar makoma ga Afrika, wanda ya kunshi neman bunkasuwa, da samar da dawwamammen cigaba, alummar Afrika masu ilmi da kwarewa, masu kuzari da koshin lafiya, zasu sauya fasalin tattalin arzikin kasashen da samar da shugabanci na gari, dukkan wadannan manyan batutuwa ne da suka bayar da gudunmawa wajen samar da muhimman abubuwan da ake bukata domin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a nahiyar. Afrika a halin yanzu tana da shekaru 43 a gabanta domin neman cimma abubuwan da kasar Sin ta cimma a cikin shekaru 35, kuma, akwai muhimman darrusa ya kamata Afrika ta koya daga irin salon da kasar Sin tayi amfani dashi wajen cimma nasarar shirin yaki da fatara wanda wani muhimmin ginshiki ne na samar da zaman lafiya da makamo mai haske. A yau, kasar Sin ta kasance babbar abokiyar huldar kasuwancin nahiyar Afrika, babbar mai zuba jari a nahiyar, Afrika ta kasancewa a sahun baya ta fuskar kasuwanci da kasar Sin, duka-duka yawan adadin cinikin da Afrika ke yi da kasar Sin bai wuce kashi 3.5% ba, idan an kwatanta da kashi 16% na kasuwancinta da EU, da kashi 10% da Japan, karuwar bukatun kayayyakin da masa'antun kasar Sin ke bukata don sarrafawa wata babbar dama ce ga Afrika da cigaban nahiyar, kasar Sin tana bukatar samun kayayyakin da masana'antu ke sarrafawa da albarkatu wadanda ake dasu birjik a nahiyar".

Dr Suleyman Ndanusa, masanin tattalin arziki kuma lauya, kana shugaban cibiyar Global Mandate Consulting dake Abuja, Najeriya, ya gabatar da lacca kan batun dorewar dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika lokacin annoba da ma bayan kawo karshen annobar COVID-19.

Dr Suleyman Ndanusa yace, yin nazari game da batun dangantakar Sin da Afrika a lokacin annoba da ma bayan annobar ta COVID-19 batu ne da ya dace kuma ya zo a lokacin da ya dace bisa lura da wannan yanayi da ake ciki.

Yace, "annobar COVID-19 al'amari ne da ya shafi duk duniya, tayi sanadiyyar haifar da karyewar tattalin arzikin duniya, ta haifar da karyewar farashin albarkatun kasa, da kuma haifar da koma baya a fannin hada-hadar kudade, nahiyar Afrika ta gamu da mumman tasirin wannan annobar, tun gabanin barkewar wannan annobar da ma akwai wasu tarin matsalolin tattalin arziki da matsalolin bashi dake damun nahiyar".

Masanin ya kuma tabo wasu batutuwa dake shafar yadda kasar Sin ke samar da rance ga kasashen Afrika, masanin yace galibin bashin da kasar ke bayarwa basu da sharruda masu matukar yawa, yace batu na biyu shine, galibin basukan da kasar Sin ke samarwa baya daukar dogon lokaci kafin a mika shi ga kasar dake bukatar rancen, batu na uku yace, kasar Sin tana da wani salo nata wanda yake matukar jan hankalin kasashen Afrika idan an kwatanta abinda mai girma shugaban kasar Sin ya bayyana cewa kasar tayi namijin kokari wajen fitar da mutane maza da mata sama da miliyan 850 daga kangin fatara, kuma karkashin dangantakar bangarorin biyu kasar Sin tana son taimakawa Afrika ta aiwatar da makamancin wannan shirin, kuma kasar Sin tana da wani salo na shirin samar da dawwamamman cigaba wanda ya sha banban da na bankin duniya da kuma asusun bada lamini na duniya wato IMF. Yace jadawalin tsarin samar da rance don raya cigaba na kasar Sin baya la'akari da yawan bashi a matsayin wata matsala da zata kawo cikas ga wata kasa wajen samun rance, a bisa ga wannan jadawalin tsarin samar da rancen na kasar Sin, ingantaccen tsarin zuba jari shine zai tabbatar da samun bunkasuwa kuma kara yawan kudaden bashi a fannin zuba jarin shine zai bada tabbacin samun bunkasuwar tattalin arzikin kasa. Masanin ya bada shawara game da matakan da zasu tabbatar da dorewar dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika bayan karshen annobar COVID-19, da daidaita ajandar bunkasa cigaba dake tsakanin Sin da Afrika, baya ga batun samar da tallafin kudi ko saukaka bashi akwai wasu matakan da zasu kara kyautata dangantakar bangarorin biyu a lokacin da ake fama da annobar da kuma bayan annobar ta COVID-19. Ya kamata a dauki matakan daidaita ajandar bunkasa cigaba ta kasar Sin da kuma ta Afrika, wannan ya zama tilas kasancewar ta hanyar tallafawa shirin samar da dawwamamman cigaban kasashen Afrika ita ma kasar Sin zata samu bunkasa a cikin gidanta. Ya kamata a daidaita alakar dake tsakanin Sin da Afrika domin ta hakan Afrikan zata iya samun damar amfana da cigaban fasahohin da kasar Sin ta samu don amfanuwa daga tsarin cin moriyar dukkan bangarorin biyu. Masanin ya karkare kasidar da ya gabatar da wasu kalamai da yace shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar inda yace:

"Zan kammala jawabina da kalaman shugaba Xi Jinping mai taken yin aiki tare domin samun cigaba na bai daya don samun makoma mai haske a nan gaba a cewar shagaba Xi Jinping kasar Sin zata aiwatar da wasu muhimman kudurori guda takwas a cikin shekaru 3 daga 2019 zuwa 2021 har ma fiye, sun hada da hadin gwiwar bunkasa masan'atu, da samar da kayayyakin more rayuwa na hadin gwiwa, da bunkasa harkokin cinikayya da samar da babban cigaba. Idan wadanan suka tabbata to ana tsammanin samun moriyar bai daya".

Shi ma Alhaji Mohammed Hayatu-Deen, wani hamshakin dan kasuwa daga tarayyar Najeriya wanda ya kware a fannonin tattalin arziki da zuba jari, ya shugabanci kamfanoni daban daban, kana shi ne mai kamfanin Alpine Investment Services Ltd, ya bayyana tasa mahangar game da tasirin da annobar COVID-19 ta yiwa nahiyar Afrika, musamman wajen karuwar talauci, da matsalolin dake shafar batun biyan haraji, da faduwar darajar kudade da matsalolin bashi. Sai dai ya zayyana wasu daga cikin matakai da yake ganin zasu taimaka wajen karfafa dangantakar kasuwanci dake tsakanin Sin da Afrika. Yace idan aka zo maganar dangantaka tilas ne a fadawa juna gaskiya ba wai domin kalubalantar juna ba sai dai domin bin matakan da za su tabbatar da dorewar dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu da kuma dorewar alaka a dogon lokaci, babu tantama Sin da Afrika sun kulla huldar dangantakar mutunta juna a tsakaninsu, amma kowace irin dangantaka tilas ne a fuskanci kalubale, wasu daga cikin matakan da zasu bayar da kwarin gwiwar dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika sun hada da yin hadin gwiwar bangarorin biyu ta fannin fasahar zamani kasancewar kasar Sin ta samu gagarumin cigaba a fannin fasahohin zamani, sannan akwai bukatar Sin ta tallafawa tsarin kiwon lafiyar Afrika sakamakon rashin ingantaccen tsarin kula da lafiyar mutanen dake cikin tsananin bukatar kulawar gaggawa, da lafiyar mata masu juna biyu lamarin dake haifar da yawan karuwar mace macen da ake samu a Afrika musamman mata da kananan yara. Masanin ya ce akwai bukatar zuba jari a fannin fasahohin kiwon lafiya na zamani domin zai taimaka wajen bunkasa cudanyar moriyar juna a tsakanin Sin da Afrika. Sannan akwai kuma bukatar Afrika ta koyi babban darasi daga barkewar wannan annoba, ya kamata kasashen Afrika su fara tunanin dogaro da junansu wajen bunkasa kasuwannin cikin gidan kasashen. Annobar ta samar da babbar dama ga nahiyar na yin tunanin bunkasa fannin masana'atu domin biyan bukatu na cikin gida a maimakon dogaro kan kasashen duniya. Ya kamata a kara martabar kayayyakin da ake samarwa a cikin gida, sannan a kara yawan hajojin da ake fitar dasu zuwa ketare. Ya ce ya kamata a yi kokarin dinke duk wata baraka a tabbatar da cike duk wani gibin kasuwanci kana a tabbatar da adalci da daidaito a tsarin mu'amalar cinikayya a tsakanin Sin da Afrika. Domin babban burin da ake da shi shi ne dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu ta dore har sama da shekaru 500 masu zuwa.(Ahmad Fagam/Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China