Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
CMG zai watsa rahoton bikin baje kolin CIIE kai tsaye
2020-11-04 14:30:42        cri

Yanzu haka, babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar (CMG) ya shirya tsaf don watsa rahotannin bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigowa da su cikin kasar Sin karo na uku kai tsaye, bikin da za a bude Larabar nan.

Darektan CMG Shen Haixiong, ya bayyana cewa, za mu yi amfani da sabbin nasarorin da muka cimma a fannin sadarwa na kasa da kasa da sabbin kirkire-kirkire a fannin kafafen watsa labarai, da goyon bayan ra'ayoyin jama'a, don samun sanar shirya bikin baje kolin karo na uku.

A halin yanzu, akwai sama da manema labarai 800 daga rukunin CMG wadanda suka shirya don sanar da duniya abubuwan dake faruwa a bikin. A lokacin bikin baje kolin, babban tashar CMG, za ta yi amfani da dukkan kafofin sadarwa, wajen watsa sabbin rahotanni, da sharhi, da gajerun hotunan bidiyo, da labarun shafuka da alamomi. Za kuma a rika gabatar da rahotanni game da sabbin hajoji na ketare kai tsaye daya bayan daya.

Bikin baje kolin, ya nunawa duniya kudirin kasar Sin da matakan da ta dauka a zahiri na ci gaba da kara bude ga kasashen ketare da gina tsarin tattalin arzikin duniya mai salon bude kofa. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China